'Yan sandan Thailand sun kama mutumin da yake safarar maniyyi

Wasu kasashe sun haramta safarar maniyyin Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Mazubin maniyyi

'Yan sandan kasar Thailand sun kama wani mutum da kananan robebi shida dauke da maniyyin dan adama zuwa kasar Laos.

Mahukunta sun samu wata jaka dauke da robobi a cikin jakar mutumin, a lokacin da yake kokarin tsallaka iyakar arewacin birnin Nong Khai a kasar Thailand.

'Yan sanda sun ce mutumin ya yi ikirarin cewa maniyyin mallakar wani asibitin haihuwa ne da ke Vietiane ,babban birnin Laos

Kasar ta Laos na fuskantar karuwar sakawa mace kwayoyin halitta domin rainon ciki, bayan kasashen Thailand da Kambodia da ke makwabtaka da ita suka haramta hakan.

'Yan sandan sun ce maniyyin na wasu maza ne 'yan kasar China da Vientiname.

Mutumin da ake zargi da fasa kwaurin ya kuma bayyana cewa ya sha kaiwa wani asibiti a Cambodia maniyyi.

Karin bayani