Koriya ta Kudu: Wani ya mutu bayan ya gama cin kwaɗo

Cin kwado ya yi ajalin wani mutum. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba a gano wane irin nau'in kwado mutumin ya ci ba., to sai dai ana zaton kwadon mai dafi ne.

Wani Mutum dan kasar Koriya ta kudu ya mutu bayan ya gama cin kwadon da yake da guba, bisa zaton cewa irin kwadon da ake ci ne.

'Yan sandan kasar sun ce, mutumin na cikin wasu mutane da suka kama kwadi biyar a wani tafki da ke kusa da birnin Daejeon, a watan jiya.

Mutumin mai shekara 57 ya fara amai jim kadan da gama cin kwadon, inda aka garzaya da shi asibiti, sannan ya mutu washe gari.

'Yan sanda sun ce, an gano akwai guba a ragowar naman da suka ci, wanda akasari ana samun irin wannan sinadarin guba na "bufotenin" a jikin kwadi.

Suma abokan mutumin da ya rasu sun nuna alamun cewa sun ci guba, to sai dai da ya ke suna da sauran kwana sun rayu.