Wasu hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Wasu zababbun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka da kuma 'yan Afirkan da suke fadin duniya a makon nan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu yin wakokin yabo sun yi ado domin gudanar da addu'o'i a coci a birnin Johannesburg dake Afirka ta kudu.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mabiya addinin Kirista dauke da itacen gicciye suna nuna alhininsu a birnin Durban a Afirka ta kudu.
Hakkin mallakar hoto Photoshot
Image caption Wani babban malamin coci yana sawa mabiyansa albarka a birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata 'yar kasar Sudan na nuna zanen da aka yi mata a fuska a wata kamar kasuwa mai nisan kilomita 480 daga babban birnin Khartoum.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu sojojin kasar Zimbabwe na gudanar da fareti, a wani bangare na bikin murnar cika shekaru 37 na samun 'yancin kasar daga Birtaniya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Alhamis ne sakataren tsaron Amurka James Mattis ya kai ziyara birnin Cairo na kasar Masar, don tunawa da wasu sojojin kasar da ba a san ko su waye ba.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hoton wata 'yar majalisa tana tafiya domin ganawa da sauran 'yan majalisu a Rabat babban birnin kasar Morocco.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu bareyi a kasar Sudan
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Laraba, mata mayaka daga kungiyar IS sun zauna domin samun horor sauya musu tunani a wata cibiya a birnin Tarabulus na Libiya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A kwanakin nan ne jami'ai suka kaddamar da wani aiki na haramta wahalar da kananan yara a kasashen da ke makwabtaka da kasar Tunisiya, wani yaro na sayar da tufafi a kasuwar babban birnin kasar Tunisiya.