An yi harbe-harbe a mahaifar Yahya Jammeh

Yahya Jammeh Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yahya Jammeh ya daga wa magoya bayansa a hannu lokacin da ya bar kasar

An yi musayar wuta a garin Kanilai, mahaifar tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh,

Sojojin tawagar kiyaye zaman lafiya na kungiyar kawancen kasashen Afrika ta Yamma, Ecowas da kuma sojin Gambia sun bude wa juna wuta.

Sojojin Ecowas sun je garin ne domin neman wasu makamai da ake zargin an boye a gidan Mista Jammeh.

Manufar Ecowas a Gambia ita ce samar da kwanciyar hankali a kasar.

Wasu majiyoyi sun shaida wa sashen Faransanci na BBC cewa, an jikkata magoya bayan Jammeh biyu, inda suke samun kulawa a asibiti.

A ranar 4 ga watan Afrilu ne tawagar sojojin Gambia da ke bakin aiki a garin Kanilai suka tursasa wa wasu daga cikin abokan aikinsu da ke sansanin sojin Yundum su dawo.

A halin yanzu Mista Jammeh na gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, bayan ya bar kasar da ya shafe shekara 22 yana mulki.

A watan Disamba ne dai kuma ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar, amma da farko ya ki bai wa Adama Barrow wanda ya lashe zaben mulki.

Labarai masu alaka