Hadarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar yara 18 a Afrika ta Kuda

Afrika ta Kudu Hakkin mallakar hoto Twitter/ER24
Image caption Akalla daliban firamare da na sakandare 20 ne suka mutu sanadiyyar hadarin mota

Masu aikin ceto a Afirka ta Kudu sun ce mutum 20 wadanda galibinsu yara ne sun rasa rayukansu sanadiyyar hadarin mota a birnin Pretoria.

Yaran sun mutu ne a lokacin da motarsu ta kama da wuta bayan da ta yi hadari da wata babbar mota a arewacin birnin.

Yaran da ke cikin motar daliban makarantar firamare da sakandare.

Jami'in da ke kula da ilimi a lardin Gauteng, Panyaza Lesufi, ya ce ''Wannan ranar bakin ciki ce a gare su.''

Motar ta ci karo da wata babban mota ne a kan hanyar R25 tsakanin Verena,Gauteng da Bronkhorstpruit da ke iyakar lardin Mpumalanga.

Har yanzu ba san abin da ya haddasa hadarin ba, amma hotuna na nuna motar ta kone tsarai.

A wata sanarwa da aka fitar, a lokacin da masu ba da agajin gaggawa na ER24 suka isa wurin, al'umman unguwan sun ceto wasu daga cikin yaran, amma sai sun mutu nan take.

"A lokacin da aka kashe wutar, an gano gawawwakin yara 13 a cikin motar.''

Ma'aikatan ER24 da Hukumar kula da ilimi a Gauteng sun tabbatar da cewa yara 18 ne suka rasa rayukansu.

Hukumar ilimi ta wallafa a shafinta na Tweeter cewa sun yi rashi sosai kuma suna cikin bakin ciki.

Afirka ta Kudu na da hanyoyi mafi hadari a duniya.

Hukumar da ke kula da sufuri ta bayyana cewa mutane 13,673 ne suka mutu cikin watanni 12 daga watan Oktoba 2015, wanda hakan ke nufin akalla mutum 37 ke mutuwa kowace rana.

Labarai masu alaka