Bayin da ba su san suna bauta ba na ƙaruwa a duniya

Wata mata na aikin buga bulo a kasar Pakistan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Galibi mata ne suka fi samun kansu cikin ƙangin bautar zamani

Wasu alkaluma sun nuna cewa sama da mutum miliyan ashirin ne ke cikin kangin bauta ta zamani a ƙasashe daban-daban na duniya.

A shekarar 1833 ne wata dokar majalisa, ta rushe duk wani nau'in bauta a faɗin Burtaniya.

Sai dai wasu masana sun yi ittifaƙin cewa bautar da aka sani shekaru aru-aru a baya, har yanzu tana wanzuwa a duniya ko da yake, a sigar zamananci.

Nau'o'in bauta na zamani da yadda za a murƙushe su na daga cikin batutuwan da waɗannan masana suka tattauna yayin wani taro a birnin London ranar Juma'a.

Malam Amir Bagwanje, ɗaya daga cikin masanan ya shaida wa BBC yadda ƙungiyarsu ta 'Media Hope' ke wayar da kai game da ƙangin bauta na zamani da illolinsa da kuma yadda za a kawo karshen matsalar.

Ya ce ɗaya daga cikin waɗannan matsaloli shi ne irin yadda akan yi fataucin ƙananan yara daga kasashen Afirka zuwa Turai, da ma wasu kasashen da suka ci gaba ta fuskar tattalin arziki.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A kan yi fataucin kananan yara daga kasashen Afirka zuwa kasashen Turai da makamantansu

A kan yi wa iyayen waɗannan yara romon-baka cewa za a nema wa yaran nasu aiki ko kuma makaranta, ta yadda za su inganta rayuwarsu, amma daga bisani sukan faɗa cikin ƙangi.

Irin waɗannan musammam mata masu ƙananan shekaru da akan ɗauko daga ƙasashensu a kan kulle su a cikin gidaje su yi ta aiki ba-ji-ba-gani, ba tare da zuwa makaranta ba.

Ba kuma tare da ana biyansu ladan wahalar aikin ba.

A lokuta da dama akan saka su cikin harkar karuwanci, ko ma iyayen gidansu su rika lalata da su.

A shekarar da ta gabata ne Fira ministar Burtaniya Theresa May ta ware dala miliyan 30 kan yaƙi da wannan matsala ta bauta.

Wannan matsala dai ba ƙasashen Afirka kawai ta shafa ba, har ma da kasashen Turai da Asia da yankin Gabas ta Tsakiya.

Labarai masu alaka