APC 'ba jam'iyya ba ce tarayyar cin mutunci ce'

Sule Lamido
Image caption Sule Lamiɗo ya ce jam'iyyarsu ta PDP ita ce ƙwaƙƙwarar jam'iyya da aka kafa a kan aƙidar haɗa kan ƙasa

Wani ƙusa a jam'iyyar adawa ta PDP ya ce ko da yake, jam'iyyarsu ta tafka kura-kurai amma APC ba mafita ba ce ga Nijeriya.

Yayin wata zantawa ta musammam da BBC, Sule Lamiɗo ya yi iƙirarin cewa APC tarayya ce ta fusatattu da mahassada da cin mutunci da wulaƙanci.

A cewarsa matuƙar PDP tana kan siraɗi to Nijeriya ma ta shiga garari. "Miƙewar PDP a matsayin jam'iyya...a kan ƙa'ida ta gaskiya, shi ne miƙewar Nijeriya."

Sule Lamiɗo ya ce babu wani tsari na ɗan'adam da babu son zuciya a cikinsa, amma ƙarfin hankali da hangen nesa da kishin ƙasa da sanin haƙƙin jama'a ne suka yi ragama.

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa yana jawabi ne a kan halin da jam'iyyarsu ta PDP ta samu kanta tun bayan faɗuwa zaɓe a 2015.

Ya ce soyayya ce da farin jini suka janyo wa PDP ɓarakar shugabanci da take ciki tsakanin ɓangaren Maƙarfi da Ali Modu Sherif.

Jam'iyar PDP kuturwar uwa ce

A cewarsa idan aka doshi shekara ta 2019, babu jam'iyyar PDP, hankalin kowa zai firgita ciki har da 'yan jam'iyyar APC. "Kowa sai ya shiga uku."

Ya yi iƙirarin cewa APC gamin gambiza ce da ba a kafa ta don (haɗin kan) ƙasa ba.

Lamiɗo ya ambato fitattun 'yan jam'iyyar APC da suka haɗar da Atiku Abubakar da Aliyu Magatakarda Wamakko da Nasiru El-Rufa'i da Rabi'u Kwankwaso, da Rotimi Amechi waɗanda ya ce duk ruhinsu na PDP.

Sule Lamiɗo ya ce Modu Sheriff da ya zo PDP daga wata jam'iyya ya shiga ne da irin hankalinsa na tafiyar da ƙaramar jam'iyya.

Ya ce akwai raini a ce Ali Modu Sheriff ya ce zai mallaki jiga-jigan 'yan jam'iyyar PDP irinsa da Adamu Ciroma da Yusuf Ayo da Goodluck Jonathan da sauransu.

Ya yi iƙirarin cewa Nyesom Wike ne da Ayo Fayose suka ɗora Ali Modu Sheriff.

A cewarsa hakan ta faru ne sakamakon ɗimuwar faɗuwa zaɓe da azabar mulkin APC na cin mutunci da kama-karya.

Sule Lamiɗo ya nanata buƙatar 'yan jam'iyyar su saki burinsu na zuciya don ɗinke ɓarakar da ke akwai, don tabbatar da makomar jam'iyyar.

Labarai masu alaka