'Yan Taliban sun yi wa sojin Afghanistan muguwar ɓarna

Afghanistan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Afghanistan na sa ido kan sansanin Mazar-e-Sharif bayan kai harin

Mayaƙan Taliban sun shammaci sojojin Afghanistan inda suka yi musu shigar burtu da kakin sojan ƙasar, a wani hari da ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 130 a birnin Mazar-i-Sharif.

Wani mai magana da yawun sojan Afghanistan Nasratullah Jamshidi ya ce 'yan tada-ƙayar-bayan sun auka wa sansanin ne lokacin da sojoji ke fitowa daga masallaci bayan kammala sallar Juma'a.

Haka kuma sun datse wasu da ke wani wurin cin abinci a sansani da ke wajen birnin Mazar-i-Sharif.

Ƙungiyar Taliban ta ce maharanta sun tarwatsa abin fashewa a ƙofar shiga, abin da ya bai wa masu harin ƙunar-baƙin-wakenta damar keta layin tsaron sansanin.

Faɗa ya rincaɓe har zuwa yammaci, yayin da jami'ai ke cewa akwai yiwuwar adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani soja na gadin harabar sansanin bayan keta layin tsaron sansanin

Akasarin mutanen da harin ya ritsa da su sojojin Afghanistan ne, amma dai an kashe wasu mayaƙan Taliban ɗin da dama.

Sansanin na Mazar-e-Sharif nan ne mazaunin rundunar sojin Afghanistan ta 209, mai alhakin tabbatar da tsaro ga akasarin yankunan arewacin kasar da suka hadar da lardin Kunduz - wanda ya yi fama da kazamin fada a baya bayan nan.

A watan da ya gabata ne aka ba da rahoton mutuwar mutum 50, lokacin da masu tada-kayar-baya na kungiyar IS suka kai hari kan marasa lafiya da ma'aikatan jinya a wani asibitin sojoji da ke birnin Kabul.

Labarai masu alaka