An ceto 'yan Turkiyyan da aka sace a Nigeria

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Nigeria police
Image caption 'Yan sanda sun ce sun kama mutum biyar

Rundunar 'yan sanda Najeriya ta ce jami'anta sun ceto 'yan kasar Turkiyyar nan biyu da 'yan bindiga suka sace a kasar.

Mutanen, ma'aikatan kamfanin gine-gine na BKS, sun fada hannun masu satar mutane domin karbar kudin fansa ne ranar 11 ga wannan watan a garin Eket na jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin kasar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Donald Awunah ya shaida wa manema labarai cewa an saki mutanen "kuma tuni aka mika su ga abokan aikinsu domin duba lafiyarsu".

Ya kara da cewa babu wanda ya ji rauni ko ya rasa ransa a lokacin da aka ceto mutane, kuma ba a biya kudin fansa a kansu ba.

A cewarsa, an kama mutum biyar da ake zargi da hannu a sace mutanen kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan batun.

Satar mutane domin karbar kudin fansa dai ba sabon abu ba ne a Najeriya.

Labarai masu alaka