MDD ta zargi Sudan ta Kudu da alhakin fadace-fadace

south sudan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya zargi gwamnatin Sudan ta Kudu da alhakin akasarin fadace-fadace a yakin basasar kasar na tsawon shekaru uku, da kuma haddasa bala'in yunwa a kasar.

Rahoton wanda wasu kwararru suka tattara, ya ce sojoji da 'yan bindiga na kabilar Dinka ta shugaba Salva Kiir ne ke kai hare-haren gwamnati.

Rahoton ya ce 'yan bindiga da sojojin gwamnatin sun rika amfani da sababbin manyan makaman da suka samu, da suka hada da jiragen helicopter.

Kwararrun Majalisar Dinkin Duniyan sun yi kiran ganin an sanya wa Sudan ta Kudun takunkumin sayan makamai, koda yake kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyan yaki amincewa da hakan a can baya.