Ana zaman makoki a Afghanistan

Kungiyar Taliban ta ce ramuwar gayya ta yi a kan kisan shugabanninta Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Taliban ta ce ramuwar gayya ta yi a kan kisan shugabanninta

Shugaban kasar Afghanistan, Ashraf Ghani, ya ayyana yau Lahadi a matsayin ranar zaman makokin wadanda harin kungiyar Taliban a wani sansanin soji da ke kusa da birnin Mazar-i-Sharif ya rutsa da su.

Sojoji da dama dai sun rasa ransu a harin, bayan da 'yan bindigar sanye da kayan soji suka shiga sansanin sojin inda suka bude wuta kan sojojin a wani gidan cin abinci, da kuma wasu dake fitowa daga masallaci.

Wasu rahotanni sun ce wadanda suka rasa ransu sun kai 140.

Mai magana da yawun 'yan kungiyar ta Taliban, ya ce harin da suka kai din fansa suka dauka a kan kisan da aka yiwa wasu shugabanninsu a kwanakin baya.

A makon da ya gabata ne, rahotannin suka ambato cewa an kashe mayakan Taliban din tara ciki har da wani babban kwamanda a kungiyar a wani hari da Amurka ta kai ta sama.

Labarai masu alaka