Ana zaben shugaban kasa a Faransa

Francoise Fillon ne daban wajen aikin gwamnati
Image caption 'Yan takara hudu ne suka fi yin fice

A ranar Lahadi ne al'ummar kasar Faransa suke kada kuri'a, a zagaye na farko na zaben shugaban kasar.

'Yan takara 11 ne dai ke neman kujerar amma takarar ta fi zafi tsakanin mutum hudu.

Zai yi wuya dai a samu mutumin da sai samu gagarimun rinjaye saboda haka sai an kai ga zagaye na biyu na zaben.

'Yan takarar hudu dai su ne Emmanuel Macron da Marine le Pen da dzon-Luc Melenchon da kuma Francois Fillon.

Francois Fillon na jam'iyyar masu raayin mazan jiya ne ya fita zakka a cikin 'yan takarar ta fannin rike mukamin gwamnati.

Francoise Fillon ya rike mukamin minista a karo da dama har kusan tsawon shekara 20.

Manyan batutuwan da suka mamaye kamfe din 'yan takarar dai su ne batun sama wa nahiyar turai makoma da al'amauran shigi da fice da tattalin arziki da kuma tantance 'yan kasa da baki.

Bisa al'adar tsarin zaben kasar, ba a samun dan takarar da zai lashe zaben da kason da ake so farat ta daya, har sai an kai ga zagaye na biyu na zaben wanda ake sa ran gudawarwa ranar 7 ga watan gobe.

Image caption An baza jami'an tsaro a Faransa

Kusan duk inda ka duba a lungu ko sakon biranen kasar Faransa, yan sanda ne da sojoji ke ta faman kai-komo a wannan rana da al'ummar kasar ke zaben shugaban da zai jaogrance su nan da shekara biyar mai zuwa.

An baza sojoji kimanin dubu 7 da 'yan sanda dubu 5 a lunguna da sako-sako na kasar.

Tun dai bayan harin da wani matashi dan asalin Afirka, Karim Shorfi mai tsananin kishin addinin Musulunci ya kai ranar Alhamis, abin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan sanda, 'yan kasar ke bacci da ido daya.

Labarai masu alaka