Neymar ba zai buga wasan Real Madrid da Barca ba

Neymar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Neymar (na baya) ya yi atisaye da Barcelona ranar Asabar, kuma mai yiwuwa a tafi da shi Madrid

Barcelona ta janye shirinta na sanya Neymar a karawar da za su yi da Real Madrid ranar Lahadi.

An dakatar da dan wasan dan kasar Brazil daga buga wasa daya a gwabzawar da suka yi da Malaga, sai dai an tsawaita dakatarwar zuwa wasa uku bayan ya yi wa alkalin wasa shagube.

Hukumar kula da kwallon kafar Spain ta ki amincewa da bukatar da Barca ta shigar ranar Juma'a kan a janye dakatarwar da aka yi wa Neymar, abin da ya sa kungiyar ta mika batun a gaban kotun wasanni ta kasar.

Kotun ta kira taron gaggawa ranar Asabar, sai dai taron bai yiwu ba saboda dukkan mambobinta ba za su iya halartarsa ba.

Kotun ta ce: "Dukkan kungiyoyin da ke buga wasa na da damar fassara hukuncin da muka yanke domin ya dace da damarsu, amma bangarorin da ke da alhakin yanke hukunci ne kawai za su amince ko ki amincewa da irin wannan batu."

Wasu rahotanni daga Spain na cewa Barca na shirin tafiya daNeymar Madrid.

A ranar Asabar Enrique ya ce: "Kungiyar nan ta yi abubuwan da suka dace sosai, wato kare martabar dan wasa. Ina ganin hakan ne ya fi dacewa. Ina shirin yin wasa ko da Neymar ko babu shi."

Labarai masu alaka