Za a ci gaba da bai wa ma'aikata alawus-alawus a Saudiyya

King Salman

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sarki Salman ya kori ministan kula da ma'aikata

Sarki Salman na Saudiyya ya mayar wa ma'aikata da sojoji kudaden alawus-alawus da aka daina biyansu a watan Satumbar da ya wuce a wani mataki na tsuke bakin aljihu bayan kudaden da kasar ke samu daga cinikin man fetur sun ragu.

Sarkin ya kori ministan kula da ma'aikatan gwamnati sannan aka soma bincikensa saboda keta ka'idojin aiki.

Kazalika ya nada dansa Yarima Khalid a matsayin sabon jakadan Saudiyya a Amurka.

Haka kuma ya kirkiri sabuwar cibiyar tsaro wadda ke karkashin kotun kasar.

Sarki Salman ya bayar da umarni a bai wa sojojin da ke bakin daga a yakin da Saudiyya take jagoranta a Yemen tukwuicin albashin wata biyu.

Yarima Khalid, sabon jakadan Saudiyya a Washington, matukin jirgin yaki ne da ya samu horo a Amurka kuma ya kai hare-hare ta sama kan mayakan IS a Syria.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kashe kusan rabin kasafin kudin 2015 wurin biyan albashi

Farashin man fetur ya tashi zuwa $52 kan kowacce ganga kuma ministocin kasar sun ce suna yawaitar da kasafin kudin bana yanzu fiye da yadda suka yi a wata ukun farkon shekarar nan.

Lokacin da farashin man ya fadi, an rage albashin ministocin da kashi 20 cikin 100 sannan aka rage kudaden biyan hayar gida da na motoci ga 'yan majalisar zartarwar kasar da kashi 15 cikin 100.