France: Le Pen da Macron za su buga a zagaye na biyu

Marine Le Pen da Emmanuel Macron Hakkin mallakar hoto AFP/EPA
Image caption Ana ganin mista Macron ne zai ci zabe

Hasashe ya nuna dan takarar jam'iyya mai matsakaicin ra'ayi, Emmanuel Macron zai fuskanci 'yar takara mai tsattsaurar ra'ayi, Marine Le Pen a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa da za a yi ranar 7 ga watan Mayu.

Wani hasashen bayan kada kuri'a ya nuna Mista Macron na da kaso 23.7 a zagayen farko na zaben, a inda ita kuma Misis Le Pen ta samu kaso 21.7.

Daman dai kuri'ar jin ra'ayin mutane tun kafin bue rumfunan zabe ta yi hasashen cewa Mista Macron zai iya kayar da Marine Le Pen a zagayen na biyu.

Wani hasashen na daban kuma ya nuna 'yan takarar biyu sun yi kankankan a zagayen farko na zaben. Nan ba da jimawa ba ne dai za a fitar da sakamakon zagayen farkon.

Yanzu haka, sakamakon da aka samu daga kaso na bisa uku na kuri'un da aka kada ya nuna Marine Le Pen ce a gaba da kaso 23.5, a inda shi kuma Emmanuel Macron yake da kaso 23. Har yanzu dai sakamakon na ci gaba da zuwa matattara.

Wane ne Macron

Emmanuel Macron ya shaida wa magoya baya cewa "Mun kawo sauyi a siyasar Faransa a cikin shekara guda."

Macron wanda tsohon ma'aikacin banki ne kuma ya rike ministan tattalin arziki a gwamnati mai ci ta Francoise Hollande kafin daga bisani ya yi murabus ya kafa sabuwar jam'iyyarsa.

Mista Macron mai shekara 39 dai bai taba tsayawa takara ba kuma idan har ya lashe zaben to zai zama shugaba na farko ma fi karancin shekaru a tarihin Faransa.

Dan takarar ya kasance yana da ra'ayin kare kimar Turawa.

Ya kuma bukaci da gwamnati ta tsame hannunta daga harkar tattalin arzikin kasar sannan kuma a janye shirin zuba jarin da gwamnatin take son yi na biliyoyin daloli.

Marine Le Pen ta jinjina wa sakamakon zabe

Jim kadan bayan da hasashen sakamakon ya fara fita, misis Le Pen ta bayyana kanta da " 'yar takara wadda jama'a ke goyon baya", a inda ta ce ci gaba da kasancewar Faransa na abun a lura sosai ne.

"An dauki matakin farko," in ji ta. " Sakamakon zaben nan abu ne mai tarihi,"

Misis Le Pen dai na jagorantar jam'iyyar Nation Front Party wadda ke adawa da 'yan cirani.

Ta yi iya bakin kokarinta wajen sassauta lafazin jam'iyyar, abin da kuma ya ba wa jam'iyyar gagarimar nasara a zaben yankuna a 2015.

Ta dai nemi da a yi wa alakar Faransa da tarayyar turai garanbawul, a inda ta kira da a kada kuri'ar raba gardama.

'Yar takarar dai na son a rage yawan baki masu kwarara cikin kasar sannan kuma a rufe masallatan masu tsaurin addini.

'Yan takara sun mara wa Macron baya

Daya daga cikin 'yan takara 11 da suka fafata kuma wanda aka yi hasashen zai kasance a sahun gaba, Francoise Fillon ya ce "babu zabin da ya dace illa a zabi mista Macron."

Hasashen da aka yi dai ya nuna Fillon na da kaso kusan 19 na kuri'ar da aka kada wato dai-dai da Jean-Luc Mélenchon.

Shi ma Benoit Hamon na jam'iyyar Socialist party ta shugaba Francoise Hollande ya ce "Ina karfafa wa kowa da kowa gwiwa wajen yakar masu matsanancin ra'ayin sassauci kuma su yi iya bakin kokarinsu wajen zabar Macron".

Kimanin 'yan sanda dubu shida da sojoji ne aka jibge a lunguna da sako-sako na kasar domin ba wa masu zabe kariya.

Tun dai bayan harin da wani matashi dan asalin Afirka, Karim Shorfi mai tsananin kishin addinin Musulunci ya kai ranar Alhamis, abin da kuma ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan sanda, 'yan kasar ke cikin firgici.

Image caption An baza jami'an tsaro a ko'ina cikin fadin kasar ta Faransa
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu tsatstauran ra'ayi sun yi zanga-zanga bayan da hasashen sakamakon farko ya fara fita