Nigeria: Abin da ya sa Buhari bai hukunta Babachir tun farko ba

Babachir Lawal Hakkin mallakar hoto Other
Image caption An dakatar da Babachir domin a gudanar da bincike kan zargin da ake masa na ba da kwangila ba bisa ka'ida ba.

Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce rashin gamsuwa da shaidar ha'incin da ake tuhumar sakataren gwamnatin kasar, David Lawal Babachir ne ya sa shugaba Buhari bai dauki mataki a kansa ba.

A makon da ya gabata ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Babachir Lawan da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar, Ayodele Oke, bisa zarge-zargen sabawa dokokin aiki da aikata cin hanci da rashawa.

Shugaban ya kuma kafa kwamitin mutum uku karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo domin bincika zarge-zargen, lamarin da wasu suke ganin akwai lauje a cikin nadi.

A baya, kafin wannan kwamiti dai shugaban ya kafa kwamiti karkashin jagorancin ministan shari'a Abubakar Malami kan batun zargin da ake yi wa Mista Babachir Lawal.

Ku saurari kashin farko na hirar da editanmu na Abuja, Naziru Mikailu ya yi da ministan shari'ar kan batun.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami