Za a fara riga-kafin malaria a Ghana da Kenya da Malawi

Maleriya Hakkin mallakar hoto D Poland/PATH
Image caption An gudanar da gwajin rigakafin a kan yara fiye 15,000

Hukumar lafiya ta duniya ta ce a karon farko za ta fara riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro a kasashe uku na Afrika da suka hada da Ghana da Kenya da kuma Malawi.

Hukumar ta bayyana cewa a shekara mai zuwa ne za a fara riga-kafin.

Kimanin jarirai dubu da dari bakwai ne ake sa ran za su amfana da allurar wanda za a debi shekaru biyu ana yi.

Shellar da hukumar ta yi ta biyo bayan wani gwaji na matakin farko da aka yi, wanda ya nuna cewa allurar ta hana mutane hudu daga cikin goma kamuwa da zazzabin cizon tsauro.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce gwajin za iya magance matsalar cutar da kashi 40 cikin 100.

Cutar malaria dai tana hallaka mutane a kalla rabin miliyan a duk shekara.

An samu ci gaba a rigakafin maleriya

• Matsalar zazzabin cizon sauro a duniya

Hukumar ta zabi Ghana da Kenya da Malawi ne saboda suna gudanar da manyan shirye-shirye na magance cutar da amfani da gidajen sauro duk da cewa kasashen na fama da cutar zazzabin cizon sauron.

Sai dai duk da nasarar da wadannan kasashe suka samu akwai wadanda ke kamuwa da cutar miliyan 212 wanda ke janyo mutuwar 429,000 mutane.

Kasashen Afrika ne suka fi fama da cutar zazzabin cutar, kuma yawancin wadanda ke mutuwa yara ne.

Karin bayani