Nigeria ta kama wiwi ta naira miliyan 400 daga Ghana

Wiwi
Image caption A dan tsakanin nan ana kama ganyen wiwi da ake shigowa da su ta hanyar ruwa

Hukumar hana fasa kauri ta jihar Lagos a Najeriya, ta ce ta kama wasu jiragen ruwa makare da ganyen wiwi da ake zargin an shigo da shi ne daga kasar Ghana.

Wannan shi ne kame mafi girma da hukumar ta yi a tashi guda a cikin shekaru biyun da suka gabata, kuma ta ce kudin wiwin zai kai naira miliyan dari hudu wato dala miliyan daya da dubu dari uku kenan.

A baya dai hukumar ta sha yin kamen miyagun kwayoyi wadanda suka hada da hodar ibilis da wiwi da dai sauransu.

Sai dai hukumar ta kama ganyen wiwi mafi yawa da ta yi zargin ana shigo da su ne daga kasar ta Ghana.

'Yan majalisa sun amince da noman tabar wiwi a Netherlands

Nigeria: An cafke ganyen wiwi na miliyoyin Naira

Shaye-shaye na kamari a Nijar

Za a halasta shan tabar wiwi a Canada

Image caption Ganyen tabar wiwin da aka kama cikin buhuhuna

Labarai masu alaka