Nigeria: Ana binciken fadar Sarkin Kano kan zargin facaka da kudin masarauta

Sarki Sanusi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya sha sukar gwamnatoci a matakan jihohi da tarayya

Hukumomi a jihar Kano da ke Najeriya sun fara binciken fadar Mai Martaba Sarkin Kanon, Muhammdu Sanusi na II a kan zargin kashe makudan kudaden masarautar ba bisa ka'ida ba.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar, Muhyi Magaji ya shaida wa BBC cewa sun samu korafe-korafe daga wajen jama'a kan zargin kashe kudaden asusun fadar da ake zargin an yi daga shekarar 2015.

"Mun gayyaci wasu daga cikin manyan ma'aikatan fadar sarki guda biyu domin su amsa tambayoyi game da wannan zargi amma babu Sarki Sanusi a cikin wadanda aka gayyata," inji Muhyi.

Sai dai bai yi karin bayyani ba kan yawan kudaden da ake magana a kai ba, wadanda rahotanni suka ce sun kai biliyoyin naira.

Amma fadar sarkin ta yi watsi da zarge-zargen, tana mai cewa basu da tushe ballantana makama.

A wani taron manema labarai da ya kira a fada a ranar Litinin, Walin Kano Mahe Bashir Wali, ya ce babu abin da aka aikata da ya saba wa ka'ida.

Ya kuma gabatar da wasu takardu da ya ce suna nuna yadda fadar ta kashe kudaden da ake magana a kai dalla-dalla kamar yadda doka ta tanada.

Sannan ya ce fadar za ta bayar da hadin kai ga binciken da hukumar yaki da cin hanci ta jihar ta fara.

Muhiyi Magaji ya ce binciken ya zama dole saboda korafe-korafen da jama'a da dama suka gabatar a gaban hukumarsa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Babu siyasa a binciken masarautar Kano - Muhyi Magaji

Ya kara da cewa "muna yin wannan bincike ne domin mu kare masarautar Kano ta hanyar gano gaskiyar lamarin domin muna wani zamani ne na dandalin sada zumunta wanda ake yada labarai daban-daban."

A cewarsa kawo yanzu wannan batu zargi ne kawai, babu wani mai laifi har sai an kammala bincike tukunna.

'Babu siyasa a cikin batun'

Binciken shi ne irinsa na farko a masarautar Kano a cikin gwamman shekaru.

Sai dai hakan na zuwa ne 'yan makonni bayan Sarki Sunusi ya soki matakin da gwamnatin jihar ta Kano ta dauka na karbar bashin kusan dala biliyan biyu daga kasar China domin gina layin dogo.

Ko da yake hukumar ta musanta cewa binciken da ta ke yi bita da kullin siyasa ne.

"Wannan ba abu ne na siyasa ba. Bincike ne da ya zama dole amma duk lokacin da irin wannan ya tashi sai ka gai mutanen suna kokarin alakanta shi da wasu abubuwan na daban," in ji Magaji.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya sha sukar gwamnatoci a matakan jihohi da tarayya

Shigar kasaita

Ya kara da cewa mun binciki mutane da dama ciki har da wadanda suke da kusanci da gwamnan jihar Kano da manyan ma'aikatan gwamnati.

Sarki Sanusi - wanda shi ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya - yana shigar kasaita da hawa motocin alfarma, kuma yana da matukar fada a ji musamman a tsakanin al'ummar Musulmi.

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya cire shi daga matsayinsa na gwamnan babban banki bayan ya yi zargin cewar gwamnati ta yi almubazzaranci da biliyoyin daloli.

Ya ci gaba da janyo ce-ce-kuce har bayan ya zama sarki.

Ya soki gwamnatin jihar Kano kan karbar rancen dala biliyan biyu daga China domin gina layin dogo.

An dan sauya wannan labarin daga baya domin gyara wani kuskure da aka yi

Labarai masu alaka