Babu siyasa a binciken masarautar Kano - Muhyi Magaji
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Babu siyasa a binciken masarautar Kano - Muhyi Magaji

Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano a Najeriya, Muhyi Magaji, ya shaida wa BBC cewa babu siyasa a binciken da hukumar ta ke yi kan korafin facaka da kudaden jama'a da ake yi wa fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Tuni dai fadar Sarkin ta musanta zarge-zargen cewa ta kashe kudade ba bisa ka'ida ba, inda ta ce a shirye take ta bayar da hadin kai game da binciken da hukumomi suke yi.

A wani taron manema labarai da ya kira a fada a ranar Litinin, Walin Kano Mahe Bashir Wali, ya ce babu abin da aka aikata da ya saba wa ka'ida.

Ya kuma gabatar da wasu takardu da ya ce suna nuna yadda fadar ta kashe kudaden da ake magana a kai dalla-dalla kamar yadda doka ta tanada.

Ga abin da Muhyi Magaji ya shaida wa Naziru Mikailu:

Labarai masu alaka