Duk wanda bincike ya biyo ta kansa ba zai sha ba - Malami

Abubakar Malami Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Malami ya ce babu sani babu sabo

Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce idan har bincike kan rashawa da cin hanci ya tarar da tsohon Shugaban kasar, Goodluck Jonathan, babu makawa za a iya bincikar sa.

Malami ya ce aikin binciken masu laifi karkashin shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari babu zabe a ciki.

Abubakar Malami ya bayyana haka a kashi na biyu na hirar da editanmu na Abuja, Naziru Mika'ilu ya yi da shi.

Ku saurari yadda hirar tasu ta kaya.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami