Boko Haram: Kamaru ta daure wani dan jarida shekara 10

Ahmed Abba dan jarida Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tuni Ahmed Abba ya riga ya shafe shekara biyu a kurkuku

Wata kotun soji a Kamaru ta yanke hukuncin shekara 10 a gidan yari ga wani jarida na sashin Hausa na gidan rediyon Faransa RFI, Ahmed Abba, bisa zarginsa da alaka da ta'addanci.

A makon jiya ne kotun ta same shi da laifin boye ayyukan ta'addanci da wanke 'yan ta'adda a rahotanninsa.

Kungiyoyin masu fafutuka sun ce Mista Abba ya yi rahoto ne kawai kan kungiyar 'yan Boko Haram.

Tun bayan samun shi da laifi kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta kasa-da-kasa mai mazauni a birnin New York na Amurka, wato Committee to Protect Journalists (CPJ), ta yi watsi da hukuncin.

CPJ ta ce ba a yi adalci ba a hunkuncin da aka yanke wa Ahmed, sanna ta nemi a gaggauta sakinsa.

A wata sanarwar da ta fitar, kwamitin ta ce " bai kamata a ce tun farko ma an tsare da kai kara da ma kama Ahmed Abba saboda aikinsa ba, balle ma har a kai ga yanke mai hukuncin shekara 10 a kurkuku".

Gidan radiyon RFI da kuma lauyansa sun ce Mista Abba, wanda ya dage kan cewa yana da gaskiya, zai daukaka kara.

Ahmed Abba ya riga ya shafe kusan shekara biyu a gidan yari.

Kamaru ta dade tana shan suka a kan tsare dan jaridar, amma hukumomin kasar sun yi burus da koke-koken da ake yi musu.

Labarai masu alaka