Nigeria: An bayar da belin jagoran 'yan Biafra Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin Nnamdi Kanui da cin amanar kasa, batun da ya musanta

Wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ta bayar da belin daya daga cikin jagororin masu fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Wannan ne karon farko da aka bayar da belinsa tunda aka fara sauraron shari'ar da ake yi masa kan zargin cin amanar kasa.

Ana tuhumar Mista Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, tare da wasu mutanen uku, wadanda duka suka musanta zargin da ake yi musu.

Mai shari'a Binta Nyako ta ce ta bayar da belin ne kan dalilan rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sharuddan belin sune sai Mista Kanu ya gabatar da mutane uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.

Mai shari'ar ta kara da cewa ba a yarda a ganshi a cikin taron jama'ar da suka wuce mutum 10 ba.

Ta kara da cewa "kar ya yi hira da 'yan jarida kuma kar ya shirya kowacce irin zanga-zanga".

Tun da farko dai Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose ya halarci zaman kotun domin karfafa wa Kanu gwiwa.

Kawo yanzu babu tabbas ko gwamnati za ta sake shi kamar yadda kotun ta bukata.

Mista Kanu ya shafe sama da shekara guda a tsare.

Labarai masu alaka