Nigeria: 'Likita ya datse' hannun wata jaririya a Kebbi

Taswirar jihar Kebbi
Image caption Gwamnatin jihar Kebbi ta kafa kwamiti don yin bincike kan lamarin

Rohatanni daga jihar Kebbi a Najeriya na cewa iyayen wata jaririya sun shiga halin zullumi sakamakon datse hannun jaririyar da wani likita ya yi, yayin nakudar haihuwarta.

Lamarin dai ya faru ne a garin Danko da ke cikin karamar hukumar Danko-Wasagu.

Wani dan uwan mahaifin jariryar ya shaida wa BBC cewa "likitan ya ce jaririyar matacciya ce sai an yanke hannunta za a iya fitar da ita".

Ya kara da cewa uwar jaririyar na cikin koshin lafiya sai dai yarinyar bata da lafiya.

Ya ce hannun jaririyar ne ya fara fitowa a lokacin nakuda kafin su isa wajen likita.

Sai dai ya ce ba zai iya tantancewa ba ko likitan yana da laifi ko bashi da shi ba.

Ya kara da cewa hakkin hukumomi ne su tantance ko likitan na da laifi ko kuma a'a, amma su ba za su dorawa kowa laifi ba.

Gwamnatin jihar Kebbi ta kafa kwamitin bincike domin tantance abin da ya faru.

A Najeriya, kamar sauran wasu kasashe masu tasowa, a kan samu kuskure a wasu lokutan da likitoci ke kokarin yin tiyata.

Labarai masu alaka