Takaddama kan matar da ta fi kowa nauyi

Eman Abd El Aty
Image caption Nauyin Eman ya kai kiligiram 500

'Yar uwar Eman Abd El Aty 'yar Masar da aka bayyana a matsayin wacce ta fi kowa kiba a duniya, ta zargi likitoci a India da karya kan lafiyar 'yar uwarta.

A cikin wani sakon bidiyo, Shaimaa Selim, ta ce 'yar uwarta, Eman Ahmed, na fama da rashin lafiya kuma ikirarin da asibitin ya yi, na cewa ta rage rabin kibarta karya ne.

A makon da ya gabata ne likitoci a asibitin Saifee da ke Mumbai, suka fitar da wani bidiyo da ya nuna cewa Eman din na zaune a kan gado.

Sun dai ce nauyinta ya ragu da kilo dari biyu da hamsin tun bayan da ta iso kasar a watan Fabrairun da ya gabata.

Likitocin sun musanta zargin kuma a cewarsu Emman a shirye take ta koma gida Masar.

Labarai masu alaka