Kotu ta tura tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu kurkuku

Mu'azu Babangida Aliyu Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Babangida Aliyu ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga shekarar 2007 zuwa ta 2015

Wata babbar kotu a Minna babban birnin jihar Naija ta tura tsohon gwamnan jihar Mu'azu Babangida Aliyu kurkuku har zuwa ranar 4 ga watan Mayu bayan da aka gurfanar da shi kan zargin aikata wasu laifuka da suka shafi kudi.

Hukumar EFCC ce ta kai tsohon gwamnan kara a gaban kotu tana zarginsa da aikata wasu laifuka lokacin da yake kan mulki.

Mai shari'a Mohammed Mayaki ya bayar da umarnin a tsare tsohon gwamnan da kuma mutumin da ya yi wa jam'iyyarsa ta PDP takarar gwamna a zaben 2015, Umar Nasko.

Duka mutanen da ake zargin sun musanta tuhumar da ake yi musu.

A farkon watan nan ne hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan, inda ya shafe kwanaki a hannunta kafin a gurfanar da shi.

Tsohon gwamnan na Neja ya shafe shekara takwas yana mulkin jihar daga shekarar 2007 zuwa ta 2015.

Kuma ya fadi takarar kujerar majalisar dattawa da ya nema a zaben 2015.

Mai shari'a Mayaki ya dage sauraron karar har zuwa ranar 4 ga watan Mayu inda zai duba batun belin da wadanda ake zargin suka nema.

Labarai masu alaka