Tattaunawa da mai safarar sassan jikin 'yan gudun hijira

Abu Jaafar

Idanuwan Abu Jaafar na cike da gadara lokacin da yake bayyana hanyarsa ta samun kuɗin shiga a rayuwa.

Yana aiki ne a matsayin mai gadin mashaya lokacin da ya hadu da gungun wasu mutane da ke safarar sassan jikin bil'adama.

Aikinsa shi ne ya nemo mutane da ke cikin halin ni-'ya-su domin su sayar da wani sashe na jikinsu, kuma kwararar 'yan gudun hijira daga Siriya zuwa Lebanon ta sa harkarsa ta buɗe.

Ya ce "Ina ci da gumin mutane, ko da yake ya nuna cewa da yawansu ka iya mutuwa cikin sauƙi a Siriya, don haka cire wani sashe na jiki ba komai ba ne, idan an kwatanta da munanan haɗurran da suka fuskanta.

"Ina ci da guminsu, amma su ma suna ƙaruwa." in ji shi.

Yana zaune ne a wani ɗan karamin shagon sayar da gahawa, a ɗaya daga cikin unguwannin mafi cunkoson da ke kudancin birnin Beirut, wani gini ne duk ya ji jiki da aka lulluɓe shi da tamfol.

A bayan ginin, wani daki ne da ke jikin wata iyaka da aka raba gidan cunkushe da tsoffin kujeru, tsuntsaye na ta kuka a cikin keji a kowacce kusurwa.

Ya ce daga nan ne ya tsara cinikin sassan jikin 'yan gudun hijira kimanin 30 a cikin shekara uku da ta wuce.

"Sun fi tambayar ƙoda, amma kuma ina iya nemowa na shirya cinikin sauran sassan jiki". in ji shi.

"An taɓa neman idon mutum, kuma na yi ƙoƙari na samo wani buƙatar sayar da idonsa."

"Na ɗauki hoton idon mutumin, kuma na aika wa masu sayen ta shafin Whatsapp don su gani ko ya yi. Daga nan, sai na kai mai sayarwar."

Ƙananan titunan da yake gudanar da harkarsa na cike da 'yan gudun hijira. Mutum ɗaya cikin huɗu na 'yan Lebanon a yanzu ya gudo ne daga tsallaken iyakar Siriya saboda rikici.

Mafi yawansu ba za a bari su yi aiki a karkashin dokar Lebanon ba, da ƙyar iyalai da yawa ke maleji.

Daga cikin waɗanda suka fi tagayyara, akwai Falasɗinawa wadanda ake ɗauka a matsayin 'yan gudun hijira a Siriya, don haka ba su cancanci sake yin rijista da hukumar kula da 'yan hgudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ba idan suka iso Lebanon.

Suna rayuwa a sansanoni masu cunkoso kuma tallafin da suke iya samu kaɗan ne.

Waɗanda suka yi kusan kamo su wajen tagayyara su ne mutanen da suka zo daga Siriya bayan watan Mayun shekara ta 2015, lokacin da gwamnatin Labenon ta ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta daina yi wa sabbin 'yan gudun hijira rijista.

"Duk wanda ba a yi wa rijista a matsayin ɗan gudun hijira ba ya shiga wahala," in ji Abu Jaafar. "To ya za su yi? Sun shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi, ba su da wata hanyar rayuwa face su sayar da sassan jikinsu"

Wasu 'yan gudun hijirar kan yi bara a tituna, musammam ƙananan yara.

Samari kuma kan yi sana'ar goge takalmi, wasu na kurɗa-kurɗa a tsakanin motoci suna sayar da cingam ko hankici, ko kuma su kare a matsayin yaran da ake bautar da su wasu su dinga ci da guminsu.

Wasu kuma kan zama karuwai. Amma sayar da wani sashen jiki hanya ce ta samun kudi na da nan.

Da zarar Abu Jaafar ya samu masu son sayarwa, sai ya ɗauke su a mota, ya rufe musu ido, zuwa wani boyayyen waje a ranar da za a cire.

Wasu lokuta likitoci kan yi tiyatar ne a gidajen haya, waɗanda aka mayar da su ƙananan asibitocin wucin-gadi, a nan ake yi wa mutum gwaje-gwajen jini kafin aikin tiyatar.

Ya ce "Da an gama tiyatar sai na mayar da mutum inda na ɗauko shi"

"Zan kula da shi har kusan mako guda, lokacin da za a cire zaren ɗinkin da aka yi. Da zarar an cire, ba ruwanmu da abin da zai faru da su".

"Ba ruwana, idan mutumin ya mutu, na samu abin da nake bukata. Ba matsalata ba ce, abin da zai faru da shi gaba matukar an biya mutum haƙƙinsa".

Abokin cinikin Abu Jaafar na baya-bayan nan, wani matashi ne ɗan shekara 17, wanda ya baro Siriya bayan kashe mahaifinsa da 'yan'uwansa a can.

Tsawon shekara uku yana zaune a Lebanon ba shi da aikin yi, ga shi ya ci bashi iya wuya, yana fama ya tallafa wa mahaifiyarsa da 'yan'uwansa mata biyar.

So, through Abu Jaafar, he agreed to sell his right kidney for $8,000 (£6,250).

To, ta hanyar Abu Jaafar, ya yarda ya sai da ƙodarsa ta dama dala dubu takwas, kimanin naira miliyan uku.

Bayan kwana biyu, ga alama yana fama da ciwo duk da magungunan da yake sha, ya kasa kwance ya kasa zaune a kan wata yagalgalalliyar katifa.

Fuskarsa ta yi sharkaf da gumi, ga kuma jini yana jiƙe bandejin da aka yi masa.

Abu Jaafar bai faɗi ko nawa ya samu a wannan harka ba. Ya ce bai san abin da ake yi da sassan jikin ba, idan an saya, amma yana jin fitar da su wasu kasashen ake yi.

Ana fama da ƙarancin sassan jikin mutum da ake buƙata don yin dashe a yankin Gabas Ta Tsakiya, saboda tasirin al'ada da addinan waɗanda za su iya ba da gudunmawar sashen jiki.

Akasarin dangi sun fi son nan da nan a binne mamaci.

Abu Jaafar ya yi iƙirarin cewa akwai aƙalla dillali bakwai irinsa da ke aiki a kasar Lebanon.

"Harka tana tafiya," a cewarsa "Harkoki gaba suke yi ba baya ba. Tabbas an samu bunƙasa bayan ƙaurar 'yan Siriya zuwa Lebanon."

Ya san abin da yake yi ya saɓa wa doka, amma ba ya tsoron hukumomi. a maimakon haka ma alfahari yake da sana'arsa. Yakan rubuta lambar wayarsa a jikin bangwayen da ke kusa.

A unguwarsu ana ganin girmansa kuma ana jin tsoronsa. Mutane kan shiga taitayinsu da zarar ya tunkari waje.

Ya cusa ƙaramar bindiga a kafarsa lokacin da muke zantawa.

Ya ce "Na san abin da nake yi ya saɓa doka, amma kuma taimako nake yi"

"Ni haka nake gani. mutumin da zai sayar da sashen jikinsa, yakan yi amfani da kudin, don neman rayuwa ingantacciya a gare shi da danginsa.

"Ya samu damar sayen mota inda yake aikin taksi, ko ma ya yi tafiya zuwa wata ƙasar.

"Ina taimakon mutane ne, ba ruwana da dwata oka"

A gaskiya ma ya ce ai dokar ce ta hana 'yan gudun hijira da yawa samun ayyukan yi da tallafi.

"I am not forcing anyone to undertake the operation," he says. "I am only facilitating based on someone's request."

"Ba na tilasta wa kowa yin haka, a cewarsa. "Ni kawai ina shiga tsakani ne idan mutum ya bukaci hakan."

Ya kunna sigari yana zare ido.

"How much for your eye?" he asks.

"Nawa za ka sayar da idonka?" ya tambaya.

Abu Jaafarba sunansa ne na ainihi ba -kawai ya yarda zai yi magana da BBC ne bisa sharaɗi za a sakaya sunsan

Labarai masu alaka