Vinod Khanna ya rasu bayan gajeruwar jinya

Vinod Khanna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Vinod Khanna ya fito a fim din Bollywood fiye da 100

Jami'an lafiya a Indiya sun tabbatar ta mutuwar daya daga cikin fitattun jaruman fim din Bollywood, Vinod Khanna, wanda ya rasu yana da shekara 70.

Mista Khanna wanda ya koma harkar siyasa ya yi fama da ciwon daji, inda aka kai shi asibiti a farkon wannan watan bayan da rashin lafiyarsa ya yi tsanani.

Ya bayyana a fim fiye da 100 na Bollywood a tsawon rayuwarsa.

An zabe shi zuwa majalisar dokokin kasar sau hudu kuma ya taba zama mataimakin ministan harkokin waje.

Mista Khanna ya fara harkar fim a shekarar 1968 kuma sananne ne a Indiya, musamman ma a shekarun 1970 da 1980 lokacin da ya yi wasu shahararrun fina-finai.

Mutane da dama na alhinin rasuwar Mista Khanna wanda ya mutu bayan rashin lafiya mai tsanani.

Masu jimami na amfai da maudu'in #VinodKhanna a shafin sada zumunta na Tweeter a kasar.

Shugaban Indiya, Pranab Mukherjee ya jagoranci 'yan siyasa da suka nuna jinjina kan rawar da Mista Khanna ya taka a fannin siyasa.

Yayin da wasu fitattun 'yan wasan Bollywood kuma ke nuna alhininsu ga mamacin.

Labarai masu alaka