Nigeria: Kun san tsarin biyan kudin aikin hajjin bana?

An gano gawa a jirgin Nigeria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An gano gawa a jirgin Nigeria mai jigilar alhazai yana mayar da su

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce a bana ba za a fitar da kudin aikin hajji na bai-daya a tsakanin jihohin kasar ba.

Shugaban hukumar, Abdullahi Mukhtar Muhammad, ya ce za a sanar da kudin hajji ne dai-dai da hidimar da kowace jihar za ta yi wa alhajinta.

Abdullahi Mukhtar ya kuma ce kawo yanzu ba a tsayar da kudin kujerar aikin hajjin bana ba.

Dangane da jin dadin alhazai, Mukhtar ya ce alhazai za su samu mahalli mai inganci kuma kusa da harami kamar yadda sauran kasashen duniya ke samu.

Ku saurari hirar Abdullahi Mukhtar tare da Aliyu Tanko:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Abdullahi Mukhtar