South Africa: An fara ƙosawa da mulkin Jacob Zuma

Ana zargin Jacob Zuma da aikata cin hanci da kuma azurta kansa da ma abokansa
Image caption Ana zargin Jacob Zuma da aikata cin hanci da kuma azurta kansa da ma abokansa

Kusan za'a iya cewa wasu 'yan kasar Afrika ta Kudu sun fara ƙosawa da shugaba Jacob Zuma, bayan zarge zargen cin hanci sun daibaibaye shi.

Ana kuma zargin sa da azurta kansa da kuma abokansa, musamman tasirin da ake gani da wasu abokan sa 'yan kasar India ke dashi wajen tafiyar da mulkin kasar.

An dai yi ta gudanar da zanga-zanga bayan da shugaban ƙasar ya sauke ministan kudin kasar, mista Gordhan daga kan muƙaminsa, mutumin da ake gani da kima a kasar, matakin da ya jefa tattalin arziki dama darajar kudin kasar cikin wani yanayi na rashin tabbas.

Matakin da Mista Zuma ya dauka na sauke Mista Gordhan daga mukaminsa ya fusata abokan adawa da kawayensa, abin da ya haddasa sabani a cikin mulkin jam'iyyar ANC, wadda ke mulki a Afrika ta kudu tun shekarar 1994.

Hakan ya sa wasu shugabanin ANC tababar ko ya kamata Mista Zuma ya ci gaba da mulkin kasar.

Magoya bayan ANC da jam'iyyar SACP da kuma babbar kungiyar kwadago ta kasar (COSATU) sun goyi bayan Zuma ya sauka da mulki.

A wata mai zuwa ne dai 'yan Majalisar dokokin kasar za su kada kuri'a na goyon baya ko kuma yanke kauna game da gwamnatin sa.

Labarai masu alaka