Kotu na taka wa Donald Trump burki kan tsare-tsarensa

Shugaban Amurka Donald Trump
Image caption Donald Trump ya tsaya kai da fata sai ya gina shinge tsakanin Amurka da Mexico

Wani babban alkali a birnin San Francisco na Amurka ya dakatar da umarnin da shugaba Donald Trump ya bayar na rike kudaden gudanarwar wasu birane da suka ki amince wa da su kama 'yan cirani domin a mayar da su kasashensu na asali.

Mai shari'a William Orrick ya nemi da a dakatar da umarnin na shugaba Trump har zuwa lokacin da za a kammala shari'ar da biranen suka kai gaban kotu.

A watan Fabrairu ne dai San Francisco da Santa Clara suka maka gwamnatin tarayyar Amurka gaban kotu kan dokar hana su kudaden gudanarwa sakamakon kin amincewa su cafke 'yan cirani.

A watan Janairu ne shugaba Donald Trump ya rattaba wa dokar da ta ba wa jihohi damar cafke 'yan cirani sannan kuma amayar da su kasashensu na asali.

Dokar ta kuma bai wa gwamnatin tarayya damar rike kudaden duk jihar ko birnin da ya ki bin umarnin cafke 'yan ciranin.

A ranar Talata ne mai shari'a William Orrick ya nemi da a dakatar da dokar har zuwa lokacin da aka kammala shari'ar.

Alkali Orrick ya bayyana dokar da wani abu mai kama da tabin hankali.

Lauyoyin masu kara sun ce kudaden da ya kamata a rike na jihohin idan har hakan ya zama dole su ne na gudanarwa ga ma'aikatun shigi da fici.

Magajin garin New York, Bill de Blasio ya jinjinawa hukuncin kotun, a inda yake fadin cewa Shugaba Trump ya nemi ya wuce makadi da rawa.

Wannan hukuncin na wucin gadi dai ana ganin kari ne a kan hukunce-hukuncen da aka yanke a baya wadanda kuma ba su yi wa Mista Trump dadi ba.

Sau biyu aka yi wurgi da dokar shugaban ta hana wasu kasashen musulmi guda bakwai shiga Amurkar.

Image caption Trump dai na son ganin an gina katangar mai tsawon mil dubu 2000

A wata dambarwar mai kama da wannan ma, shugaba Donald Trump ya yi amai ya lashe dangane da batun yi wa Amurkar shinge tsakaninta da Mexico.

Wannan batu dai na daya daga cikin manyan alkawuran da ya lashi takobin aiwatarwa idan ya hau karaga, a lokacin yakin neman zabensa.

Daman dai 'yan majalisar dokokin kasar na jam'iyyar Democrat sun sha alwashin yi wa kudirin kutungwila idan har ya zo gabansu.

Za dai a iya cewa firgicin da kalaman mista Trump suka jefa al'ummar Amurka da duniya lokacin yakin neman zabensa, sun fara zama fadi ba cikawa.

Labarai masu alaka