Nigeria: Yadda Oba na Legas ya 'wulakanta' Ooni na Ife

Adeyeye Ogunwusi, ooni na ife Hakkin mallakar hoto OONI FACEBOOK GROUP
Image caption Ooni na Ife shi ne gaba da Oba na Legas a tsarin sarautar kabilar Yarbawa

'Yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani a kafafen sada zumunta bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda Oba na Legas ya ki gaisawa da Ooni na Ife a bainar jama'a.

Oba Rilwan Aremu Akiolu, mai shekara 73, ya ki mika hannu domin gaisa wa da Ooni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi, mai shekara 42 a lokacin wani taro a birnin Legas.

A bidiyon da ake yada wa a shafin Twitter, a lokacin da Ooni na Ife ya shiga dakin taro ya mika wa Rilwan hannu don su gaisa amma maimakon hakan, sai kawai ya daga masa hannu ya ki yarda su yi musabaha.

Bayan Akiolu ya ki mika wa Ogunwusi hannu su gaisa, sai kawai Ooni na Ifen ya juya ya koma inda aka ajiye masa kujerarsa ya zauna.

A kabilar Yarbawa dai ana yi wa Ooni na Ife kallon sarkin sarakuna kuma shi ne gaba da Oba na Legas.

An nada Mista Ogunwusi ne a baya-bayan nan, yayin da Akiolu ya shafe dogon lokaci a matsayin Oba na Legas.

Jama'a a Twitter dai sun yi Allah-wadai da abin da Oba na Legas din ya yi:

Ugochukwu Azonobi ya ce: "Ya kamata a gaya wa Oba na Legas cewa Ooni tsatson Oduduwa ne kuma ba sa'ansa ba ne".

Yayin da Olajohn Olutumi ya ce: "Ban san abin da ya faru ba, amma koma mene ne, bai kamata Oba na Legas ya yi haka ba. Ya nuna rashin dattaku".

Hakkin mallakar hoto Twitter

Labarai masu alaka