Matar da ke so 'yan China su rika cin kwari

Matilda Ho Hakkin mallakar hoto RYAN LASH/TED
Image caption Matilda tana so ta yi amfani da fasaha wajen inganta yadda mutanen China ke cin abinci

Wata 'yar kasuwa a China ta fara amfani da hanyoyin kasuwanci na intanet domin tallata na tallata wa mutanen kasar wasu kwari a wani kamfe na inganta yadda 'yan kasar ke cin abinci.

Matilda Ho ta yi jawabi a wurin wani taron fasaha da tsare-tsare na Ted a kan bukatar yada manufarta a kan cin abinci mai gina jiki.

Mutane da dama a China na fama da matsalar matsananciyar kiba da ciwon siga.

Misis Ho ta shaidawa BBC cewa "yawan mutanen China sun kai kashi 20 cikin 100 na yawan mutanen da ke duniya amma kuma kashi 7 cikin 100 na gonakinsu ne kawai ake iya nomawa".

Ta kara da cewa daya daga cikin mutum hudu masu ciwon siga dan China ne, haka zalika daya daga cikin mutum biyar na masu kiba sosai daga kasar ne.

Misis Ho ta fara magance matsalar ne ta hanyar samar da kasuwar manoma ta intanet wadda ke samar da sabbin kayayyakin abinci daga manoma 57.

Mutum 40,000 na bibiyar kasuwar intanet din tun da aka kaddamar da ita watanni 18 da suka gabata.

"Ina so na yi amfani da fasaha wajen takaita gibin da ke tsakanin masu samar da abincin da masu saye," kamar yadda ta shaida wa BBC.

"'Yanci ne kasan daga ina ake samar da abincin da kake ci kuma hakan yana karfafawa mai saye gwiwa."

Ana aike wa masu sayan kayan abincin na su ta motocin lantarki a cikin kwalayen da za su hana su lalacewa.

Misis Ho ta ankara cewa ba a da isassun kananan sanao'i na intanet don haka yanzu ta kaddamar da abin da zai bunkasa cigaban wasu kamfanonin da ke kirkirar fasahar abinci.

"A China, masana'antun da ke yin tufafi na amfani da tsutsar silkworm don haka suna da arha kuma suna da saukin samu kamar yadda Ho ta bayyana.

Ta kara da cewa "ba a cika kyankyaminsu kamar yadda ake yi wa kwari ba. Da muna yara mun yi kiwon tsutsar Silkworm a makaranta."

Akwai tarihin cin tsutsa a China amma a yanzu tsutsotsin silkworm kawai aka halasta amfani da su a matsayin wani sinadarin hada abinci.

Labarai masu alaka