Kim Jong-un zai dandana kudarsa a hannun Amurka

Jirgin ruwa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amurka ta aike da jiragen yaki na ruwa da jiragen karkashin ruwa zuwa zirin koriya

Babban kwamandan rundunar sojin Amurka da ke Pacific ya ce na'urorin kare kai daga makami mai linzami da ke Korea ta kudu za su sanya shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un ya shiga hayyacinsa ba wai a durkusar da shi ba.

Adm Harry ya shaida wa majalisar dokokin Amurka cewa Amurka za ta kasance a shirye da "fasahar zamani" domin ta murkushe duk wata barazanar makami mai linzami daga Koriya ta arewa.

Adm ya shaida wa kwamitin soji da ma'aikatar tsaron Amurka cewa Mista Kim na ci gaba da matsayawa kusa da manufarsa ta amfani da makaman Nukuliya a biranen Amurka.

Ya kara da cewa "kamar yadda shugaban Amurkan, Donald Trump da sakataren tsaron kasar James Mattis suka fada, duk hanyoyin da za mu tunkari kasar a bude suke".

Amurka ta aike da jiragen yaki na ruwa da jiragen karkashin ruwa zuwa zirin koriya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amurka zata kasance a shirye da " fasahar zamani" domin su murkushe duk wani barazanar makami mai linzami daga Koriya ta arewa.

China na ganin cewa tsarin makami mai linzami na Thaad na Amurka zai hargitsa yanayin tsaro.

Ana ci gaba da samun tashin hankali a dai dai lokacin da ake zaman dar dar kan cewa ta yiwu Koriya ta Arewa na shirin gwajin wasu makamai masu linzami da makaman Nukuliya.

A lokacin da yake wani bayani gabanin wata tattaunawa ta sanatoci a fadar White House, Adm Harris ya ce ya yi amannar cewa Koriya ta arewa za ta yi kokarin kai wa Amurka hari da zarar ta samu karfin sojin da take bukata.

Labarai masu alaka