Masu sana'o'i a birnin Kumasi

A ranar 6, ga watan Mayun shekarar 1957, kasar Ghana wacce a baya aka santa da cinikin zinare, ta samu 'yancin kai daga Turawan Birtaniya.

A bikin cika shekara 60 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, wani mai daukar hoto, Ricky Darko ya yi duba da garin da aka haife shi wato Kumasi, a kudancin kasar, don nuna ire-iren ayyukan da matasa suke da damar samu a lokacinsa.

Birnin Kumasi Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Birnin kumasi da ke Ghana

A lokacin da Darko ke bikin cika shekaru 30 da haihuwarsa, ya kira samari sa'anninsa da su fito su dauki hotuna a wuraren da suke aiki.

Ya hadu da abokan nasa a ranakun da suke gudanar da aikinsu, inda ya tarar da kowanne yana da fannin da ya kware a sana'arsa, wanda yawanci sun gada ne daga wurin iyaye da kakanni.

Daga cikin kanikawan da suke aikin kere-kere, yawancin mazan suna aiki tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta, cikin zafin rana da ya kai maki 35 na ma'aunin Selsiyos.

Darko ya ce, yadda suke gudanar da rayuwarsu sai san barka.

ya ce, suna yin aikinsu da kwazo na tsawon sa'o'i a cikin yanayin zafi amma ba tare da yin korafi ba.

David yana daya daga cikin samarin da ya ci karo da su.

Ya zagaya cikin Kumasi yana yin ayyuka daban-daban tun daga kwashe bola zuwa kai ruwa gidaje.

David,mai kaya a Kumasi Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption DavidYa zagaya cikin Kumasi yana yin ayyuka daban-daban

Kwame ya leko waje ta tagar motar da yake ciki mai launin azurfa, wacce ake aikin da ita a gidan attajiran da yake yi wa aiki.

A wannan ranar ne, zai dauki iyalansa don ziyartar abokai, sannan su wuce kasuwa su sayi kayan masarufi don amfanin yau-da-kullum.

Kwame na zaune a motarsa Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Kwame ya leko waje ta tagar motar da yake ciki mai launin azurfa
Kumasi, Ghana Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Ghana wacce a baya aka santa da cinikin zinare,

Nana Kwasi da ke zaune a kan Bonnet din motarsa, ya shaida wa Darko cewa yana biyan kudin balas na hayar motarsa a kan cedi 40 na kudin Ghana a kowacce rana.

Sannan ya zagaya cikin garin Kumasi, dan ya yi kokarin samun isasshen kudin da zai tallafa wa iyalansa.

Wani na tsaye kusa da motarsa Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Nana Kwasi da ke zaune a kan Bonnet din motarsa,

Akwasi na tsugune a kusa da kofofin karfe da ya kera.

Garejinsa na kusa da gidaje, kuma yana aikin waldan kayayyaki daban-daban da 'yan kasar Ghana ke amfani da su.

Akwasi Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Akwasi na tsugune a kusa da kofofin karfe da ya kera.
wani mai aikin walda Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Wani mai aikin walda
Francis na waldar kofa Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Francis na aikin waldar karafuna

Francis yana aikin ne a matsayin mai sayar da kayayyakin cimaka, galibi ya fi sayar da alewa a kan titinan cikin gari da motoci suke yawan wucewa.

Ya ce, Suna gudanar da cikakkiyar rayuwarsu kuma duk lokacin da suka ganni suna min dariya, a matsayi na na wanda nake kokarin yin magana da harshen Twi (wani yare ne a harshen Aka, wanda yawancin ake magana da shi a kudancin Ghana).

Darko ya ce, ina jin harshen ba dadi, idan na cakuda shi da kalmomina.

Francis Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Wani saurayi

Wadannan samarin 'yan uwan juna ne ke zaune a kofar shagonsu, inda suke sayar da kayayyakin amfanin gida.

Yaw daga hagu, Poku a dama, suna gudanar da harkokin cinikinsu na tsawon sa'o'i 16 a rana.

Two men sit outside a stall Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Yaw (daga hagu), tare da Poku, suna zaune a shagonsu
A roadside hut in Kumasi, Ghana Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Wasu kayayyaki a Kumasi.

Emmanuel na aiki dare da rana a matsayin mai gadin wasu kayayyaki a Kumasi.

A karshen mako ne kawai, yake samun sa'o'i uku, don ya zauna tare da iyalansa.

Emmanuel, mai gadi Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Emmanuel na aiki dare da rana a matsayin mai gadi

Michael na sayar da katin waya, a cikin wani dan akwati da aka kera da katako, da ruwan leda a cikin kula.

Michael, mai sai da katin waya Hakkin mallakar hoto Ricky Darko
Image caption Michael na sayar da katin waya

Dukkan wadannan hotunan mallakar Ricky Darko ne.