Ana binciken jirgin sama a kan mutuwar zomo

Simon the rabbit Hakkin mallakar hoto CATERS NEWS
Image caption Ana zaton Simon zai zama zomon da ya fi kowanne girma a duniya.

Kamfanin jiragen saman United Airlines na kasar Amurka na gudanar da bincike kan mutuwar wani babban zomo, wanda aka dauka a cikin daya daga cikin jiragensu.

Zomon mai tsawon santimita 90, da ake kira da Simon, an same shi a mace a cikin kayan jirgi a lokacin da jirgin ya sauka a filin saukar jiragen sama na O'Hare Chicago wanda ya taso daga filin jirgin saman Heathrow da ke Landan.

Rahotanni daga kafofin watsa labaran Amurka sun ce, babban zomon mai wata goma wanda aka tafi kaiwa wata sabuwar uwargijiyarsa.

Amurka - wacce ta kasance cikin matsanancin halin munanan tallace-tallace na wasu 'yan makonni - ta ce ta yi matukar bakin-ciki da mutuwar Simon.

Ba a fiya samun mutuwar dabbobi a jirgi ba.

Sashen kula da harkokin sufuri na kasar Amurka, ya nuna cewa bayanan da aka samu na baya-baya nan a shekarar 2015, Kamfanin jiragen saman Amurka sun ba da rahoton mutuwar dabbobi.

Hakkin mallakar hoto CATERS NEWS
Image caption Annette Edwards ta rike zomonta mai suna Darius

A wata sanarwa da aka turawa BBC, inda Amurka ta ce, "Mun yi matukar bakin-ciki da jin wannan labari". Samun cikakkiyar kulawa da tsaro na dukkan dabbobin da za su yi tafiya da mu abu ne mai matukar muhimmanci ga Kamfanin jiragen saman kasar Amurka.

"Muna da kyakkywar alaka da abokan huldarmu,kuma muna basu taimako. muna bibiyar wannan al'amari.

Jaridar Sun ta kawo rahoton cewa, Simon mai wata 10 dan zomon da ya fi kowanne zomo girma a duniya, wanda tsawonsa ya kai 1.3m babban zomon da ake kira Darius, kuma ana tsammanin zai yi girma fiye da babansa.

Annette Edwards, wacce ita ce mai zomon, ta shaida wa jaridar cewa, "Sa'o'i uku kafin su shiga jirgin likitoci sun duba lafiyar Simon kuma an tabbatar da lafiyarsa inda suka ce zai iya tafiya da shi a matsayin abin wasa."

"Wani bakon al'amari ya faru kuma ina so na san menene. Na sha tura zomaye a fadin duniya amma irin haka bai taba faruwa ba a baya," in ji ta.

Labarai masu alaka

Karin bayani