Hare-haren kunar bakin wake sun kashe mutane a Maiduguri

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram ta kara kaimi wajen kai hare-haren kunar bakin wake ne bayan sojojin Najeriya sun fatattake ta daga dajin Sambisa

Wasu jerin hare-haren kunar bakin wake sun kashe mutum biyar a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wadanda suka mutu a hare-haren sun hada da 'yan kunar bakin wake hudu da kuma wani dan kato da gora, wato Civilina JTF.

Jami'ai sun ce an kai wadanda suka ji rauni a harin asibiti yayin da hukumar ba da agajin gaggawar a jihar ta ce za ta ci gaba da tallafawa wadanda abin ya rutsa da su.

Rahotanni sun ce an ci gaba da harkoki a birnin kamar yadda aka saba.

Kungiyar Boko Haram ta koma amfani da mata da yara wajen kai hare-haren ta'addanci kan cibiyoyin farar hula tun bayan dakarun Najeriya suka fatattake su daga dajin Sambisa.

Labarai masu alaka