'Yan sanda sun kwace takardun kasafin kudin Nigeria - Goje

Mohammed Danjuma Goje Hakkin mallakar hoto Nigerian Senate
Image caption Kawo yanzu dai 'yan sanda ba su fito sun ce uffan ba kan samamen na gidan Sanata Goje

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawan Najeriya, Danjuma Goje, ya ce za a jinkirta kasafin kudin kasar na bana domin 'yan sanda sun kwace wasu muhimman takardu a gidansa.

Sanata Goje ya fadi haka ne a zauren majalisar inda ya ba wa takwarorinsa labarin samamen da 'yan sanda suka kai gidansa da ke Abuja a makon jiya.

Sanatan mai wakiltar Gombe ta tsakiya ya ce kasafin kudin da kwamitinsa ke aiki a kai na cikin kwamfutocin da 'yan sanda suka dauke a lokacin da suka kai samamen.

Bayan ya saurari koken Goje, Shugaban majalisar Bukola Saraki ya mika batun ga kwamitin wucin gadin da majalisa ta nada don bin bahasi kan zargin yunkurin kashe Sanata Dino Melaye.

Wannan batu ka iya kara kawo cikas ga kasafin kudin na bana, wanda tuni aka samu jinkiri wurin amince wa da shi.

Kasasfin kundin na shekarar 2017 dai sai ya samu amicewar bangaren majalisar biyu kasar kafin ya zama doka.

A makon jiya ne 'yan sanda suka kai samame gidan Sanata Goje da ke unguwar Asokoro a Abuja.

Rahotanni sun ce sun awangaba da kudade da kuma wasu kayayyaki daga gidan.

Kawo yanzu dai 'yan sandan Najeriya ba su fito sun ce wani abu ba game da samamen.

Labarai masu alaka