Me kuke son sani game da jam'iyyar APC?

APC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption APC ta karbi mulki daga PDP a 2015

A watan gobe ne jam'iyyar APC da ke mulkin Najeriya ke cika shekara biyu da soma mulki bayan ta kayar da jam'iyyar PDP, wacce ta shekara 16 tana mulki, a zaben 2015.

Wasu na ganin jam'iyyar ta APC ta taka rawa sosai wajen kawo sauyi a shekaru biyun da ta yi a kan mulki, yayin da wasu ke cewa gara jiya da yau.

Bangarori daban-daban, wadanda suka hada da jam'iyyar CPC da jam'iyyar ACN da kuma gyauron 'yan jam'iyyar PDP, ne suka dunkule wuri daya suka kafa APC, lamarin da ya sa masana siyasa ke ganin har yanzu zaman 'yan marina ake yi a jam'iyyar shi ya sa ma ta kasa gudanar da babban taronta.

Sai dai manyan jami'an jam'iyyar sun ce bakinsu daya, kuma suna aiki ne domin ci gaban kasar.

Me kuke son sani game da wannan jam'iyya ta APC, musamman kan shugabancinta?

Ku aiko mana sako a cikin wannan akwatun da ke ƙasa.

Mun daina karbar tambayoyi ta wannan shafin. Mun gode.

Labarai masu alaka