'Fasa-ƙwaurin shinkafa ya durkusar da kasuwancinmu'

Manoman shinkafa a Najeriya
Image caption Masu sarrafa shinkafa a Najeriya sun koka da shigo da shinkafa daga waje

Masana'antun shinkafa a Nijeriya sun koka a kan koma-bayan kasuwa da shinkafar da suke sarrafawa a cikin gida take fuskanta saboda fasa-ƙwaurin ta ƙasashen waje da ake yi.

Sun bayyana fargabar cewa burin gwamnatin ƙasar na wadata Nijeriya da shinkafa a nan kusa ka iya zama mafarki, inda suka yi zargin cewa masu fasa-kwauri da hada baki da jami`an kwastam wajen satar shiga da ita ƙasar.

Wannan lamari dai a cewarsu, ya sa kasuwar shinkafar gida ta faɗi, abin kuma da ke tilasta rufe masana`antun.

Gwamnatin Nijeriya a baya-bayan nan ta ɓullo da matakai iri daban-daban don bunƙasa noman shinkafa a cikin gida.

Daga ciki har da bai wa manoma da masu masana'antun sarrafa shinkafa kariya ta hanyar taƙaita shigar da ita daga ƙasashen waje.

Sai dai, a baya bayan nan masu sarrafa shinkafar da kasuwancinta sun ce suna fuskantar barazanar da ka iya gurgunta musu sana'a.

Injiniya Nazifi Ilyasu shi ne kakakin kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nijeriya kuma ya shaida wa BBC cewa yanzu kasuwancin shinkafa ta cikin gida, ba ya tafiya.

Ya kuma yi zargin cewa: '' Ana shigo shinkafar kasashen waje sosai ta wasu kan iyakokin Nijeriyar, tana neman ta taɓa harkar masana'antunmu''

Image caption Shiga da shinakafar waje na kashe wa ta gida kasuwa a cewar masu masana'antu

Masu shinkafar dai sun koka kuma da cewa rashin cinikin ya sa farashin shinkafar na faɗuwa.

Binciken da BBC ta gudanar ya gano cewa akwai masana'antun sarrafa shinkafa da dama da suka rufe aiki a yankin jihar Kano.

Amma kuma a ɓangaren 'yan kasuwa sun ce rangwamen farashi ne ke sa shinakafar waje kashewa ta gida kasuwa.

Alhaji Uba Zubairu Yakasai shugaban kasuwar kwanar Singer ta Kano, ya ce shinkafar gida ta fi ta waje tsada shi ya sa ake sayen ta fiye da ta gida.

Ya kuma ce ta gidan idan farashinta ya yi ƙasa babu abin da zai sa mutane su sayi ta waje.

Hukumar Kwastan ta Najeriya a nata bangaren ta ce tana da labarin fasa-ƙwaurin shinkafar amma bai yi munin da zai sa shinkafar waje ta mamaye kasuwannin kasar ba.

Ta kuma musanta cewa ana haɗa baki da wasu jami'anta wajen shigar da shinkafar daga waje.

Labarai masu alaka