An saye wani ƙauye da aka yi wa kuɗi fam miliyan 20

West Heslerton Hakkin mallakar hoto CUNDALLS
Image caption Ƙauyen West Heslerton na da nisan kilomita 9 daga Malton a Yorkshire ta Arewa

An sayar da wani ƙauye sukutum, da aka sa shi a kasuwa cikin shekara ta 2016 a kan kuɗi fam miliyan 20 a Ingila.

Ƙauyen West Heslerton, da ke kusa da yankin Malton, na da wani danƙareren gida mai ɗaki 21, da mashaya da gidan mai da gida 43 a kan fili mai faɗin eka 2,116.

Dangi guda ne suka mallaki ƙauyen tsawon sama da shekara 150, kuma an sa shi a kasuwa bayan mutuwar wanda ya mallake shi na baya-bayan nan.

Kamfanin hada-hadar gine-gine na Cundalls ya ce wani kamfani mai harkokin noma da zuba jari a Norfolk Albanwise ne ya saye ƙauyen West Heslerton.

Hakkin mallakar hoto CUNDALLS
Image caption Ƙauyen na da wani tamfatsetsen gida mai ɗaki sama da 20 a cikinsa.

Wani mai magana da yawun kamfanin ya ce Albanwise na daf da kammala ciniki a ranar Juma'a kuma tuni ya fara ganawa da 'yan ƙauyen

Ba a dai bayyana ko nawa kamfanin ya biya don saye ƙauyen ba.

A shekarar 1960 ce Eve Dawnay ta gaji rukunin gidajen ƙauye, amma sai makusantanta suka yanke shawarar sayar da shi bayan ta rasu a shekara ta 2010.

A lokacin da aka sa ƙauyen a kasuwa, mutanen ƙauyen sun bayyana lamarin da cewa "ƙarshen zamani".

Ita dai Eve Dawnay ta yi suna a kan rashin tsawwala kuɗin haya, abin da kamfanin Cundalls ya ce ya taimaka wajen bunƙasa harkoki a ƙauyen.

Labarai masu alaka