Ministan labaran Nigeria ya yi amai ya lashe

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Tun bayan dawowarsa daga jinya a Ingila ne, shugaba Buhari ya rage fitowa bainar jama'a

Ministan yaɗa labaran Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed ya ce shugaban ƙasar zai yi aiki a gida ranar Laraba, amma ba daga yanzu zai riƙa aiki daga gida ba.

Wata sanarwa da ministan ya fitar ta ambato shi yana cewa wasu kafofin yaɗa labarai sun yi wa bayanin da ya yi, kuskuren fahimta.

A cewar sanarwar ministan bai taɓa cewa nan gaba shugaban Nijeriya zai riƙa aiki ne daga gida ba.

Ta ce kanun da wasu kafofin yaɗa labarai suka buga cewa "Daga yanzu Buhari zai riƙa aiki daga gida" bahaguwar fahimta ce aka yi wa kalamansa a wata tattaunawa da 'yan jarida.

Jawabin dai ya tayar da hankulan 'yan Nijeriya inda wasu ke bayyana fargaba game da halin da lafiyar Muhammadu Buhari take ciki.

Sai dai a wani sautin kalaman ministan da aka naɗa lokacin da yake jawabi ga manema labarai, an jiyo shi yana cewa shugaban ƙasa zai riƙa aiki ne daga gida.

"A kai masa duk fayel-fayel ɗinsa gida"

Yayin taron 'yan jaridar, Alhaji Lai Mohammed ya ce na tabbata kun lura cewa shugaban ƙasa ba ya nan.

Ba ya nan ne saboda ya ce a bar shi ya huta, don haka ya buƙaci mataimakinsa ya jagoranci taron (Majalisar Zartarwa), in ji shi.

"Kuma zai riƙa aiki ne daga gida. Ya ce ma a kai masa duk fayel-fayel ɗinsa zuwa gida."

A cewarsa, mai yiwuwa ne mataimakin shugaban ƙasa zai gana da shugaban ƙasa nan gaba a yau don tuntuɓa.

Tun bayan dawowar shugaba Muhammadu Buhari daga jinyar kwana 50 ne, aka daina ganinsa a bainar jama'a.

Karo uku kenan a jere, shugaban na Nijeriya bai halarci taron Majalisar Zartarwar ƙasar na mako-mako da ya saba jagoranta ba.

Labarai masu alaka