Ana binciken wani malami a Malaysia kan mutuwar Almajirinsa

Makarantar addini Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES
Image caption Yaron na zuwa makarantar mai zaman kanta, wacce daya ce daga cikin irinta masu yawa a kasar

'Yan sanda a Malaysia na binciken mataimakin shugaban wata makarantar Islamiyya kan laifin kisan kai bayan mutuwar wani dalibi da ya zane.

Ana zargin malamin da laifin dukan Mohamed Thaqif Amin mai shekara 11, da robar ruwa.

Daga baya yaron ya kamu da ciwo mai tsananin, inda likitoci suka yanke kafafunsa.

A ranar laraba ne, ya mutu sakamakon fama da matsanancin ciwo.

Lamarin dai, ya janyo kiraye-kirayen akan gudanar da bincike kan makarantun addini.

Me ya faru da yaron?

A karshen watan Janairu ne, yaron ya shiga makarantar Islamiya mai zaman kanta dake garin Kota Tinggi, a jihar Johor.

'Yan sanda sun ce yaron daya ne daga cikin yara 15 da malamin ya yiwa duka a ranar 24 ga watan Maris saboda laifin surutu.

Rahotonni sun nuna cewa mahaifiyarsa ta fitar da shi daga makarantar bayan da ta kai ziyara a makarantar kwanakin bayan haka ya faru, kuma ta same shi baya jin dadi sosai.

Hakkin mallakar hoto Image copyrightAFP/GETTY IMAGES
Image caption Akwai dubban makarantun Islamiya a kasar

An kai shi asibiti bayan makonni uku da kafafuwansa suka fara kumbura saboda taruwar jini da ya hana jini zagayawa cikin jikinsa.

Da likitocin suka lura cewa wurin kamu da cututtuka masu tsanani, sai suka yanke kafafuwansa.

Suna shirin yanke hannusa na dama ne a ranar Laraba da ya rasu.

Da farko dai, 'yan sanda sun cafke mataimakin shugaban makarantar, wanda bai bayyana sunansa ba,da laifin cin zarafin yara amma sun ce zasu sake binicikensa akan kisan kai bayan mutuwar Mohamed Thaqif.

'Yan sanda sun kara da cewa an taba tsare shi a kurkuku saboda laifin sata.

Makarantar dai, taki bada nata jawabi da cewa 'yan sanda na gudanar da bincike akan lamarin.

Hukumar makarantar Johor ta gudanar da nata bincike inda ta ce makarantar bata yi laifi ba.

Amma shugaban makarantun addini a kasar ya ce hotuna daga CCTV, sun nuna cewa "ana dukan daliban akan kafa daya kadai" don haka akwai yiwuwar hakan ya haifar da wannan matsala ga yaron.

Wannan lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan kasar, inda suke tambayar dalilin da ya sa makarantar ta dauki mutumnin da aka taba samu da laifi ya kula da yaransu kuma ya aka yi ba a lura yana cin zarafin yaran ba?

Firayin ministan kasar, Najib Razak, ya yi kira da a gudanar da bincike na gaggawa akan lamarin

Labarai masu alaka