Hissene Habre zai fuskanci daurin rai da rai

Hissene Habre Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hissene Habre shi ne tsohon shugaban kasa a Afrika na farko da aka taba yankewa hukunci a wata kotun da AU ke goyawa baya

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Senegal ta tabbatar da hukunci daurin rai da rai da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre.

A bara ne dai wata kotu ta musamman da kungiyar tarayyar Afrika ta kafa ta samu Habre da laifukan da suka hada da keta haddin bila'ama da laifukan yaki da azaftarwa da fyade tare da ba da umarni ayi kisa.

Lamarin dai ya faru ne a umarni a yi kisa a lokacin da ya ke kan mulki a Chadi a shekarun 1982 zuwa 1990.

Haka kuma kotun ta bukaci ya biya diyyar miliyoyin daloli ga wadanda abin ya shafa.

Tsohon shugaban Chadin mai shekaru 70 a duniya ya ki amincewa da kotun kuma bai yi magana ba a yayin zaman kotun ta musamman.

Habre dai yana zaman gudun hijira ne a Senegal a lokacin da aka damke shi bayan gwamnatin kasar ta fuskanci matsin lamba daga kasashen yamma da kuma iyalai da 'yan wadanda lamarin ya shafa.

Labarai masu alaka