El-Rufai da Saraki ne suka hana ni zama mataimakin Buhari —Tinubu

Bola Tinubu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bola Tinubu na cikin wadanda suka mara wa Buhari baya a zaben 2015

Daya daga cikin jagororin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya kuma tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya ce Shugaban Majalisar Dattawan kasar, Bukola Saraki, da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, su ne suka hana shi zama mataimakin Shugaba Buhari.

Jaridar Punch ta ambato cewa a littafin shugaban hukumar editocin jaridar This Day, Olusegun Adeniyi, mai suna 'Against The Run of Play' Tinubu ya ce 'yan siyasar biyu ne suka hana shi zama abokin takarar Shugaba Buhari a zaben 2015.

A cewar Tinubu, El-Rufai da Saraki sun yi ta nanata wa Buhari da kuma 'yan jam'iyyar cewar idan aka hada 'yan takara biyu Musulmai, jam'iyyar ba za ta kai labari a zaben ba.

Tsohon gwamnan na Legas ya ce sun kaddamar da kamfae din hana shi zama abkoin takaran Buhari ne a boye duk da cewar duk abubuwan da jam'iyyar ke yi ana yin su ne a idon kowa.

Ya ce Nasir El-Rufai ya so Buhari ya dauko Pasto Tunde Bakare, wanda suka yi takara da Shugaba Buhari a zaben 2011 a karkashin jam'iyyar CPC.

Tinubu ya ce ya janye bukatarsa ta zama abokin takarar ne domin ya mika sunan farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ya taba ambata wa shugaban a shekarar 2011.

Wannan labarin ya kara haske kan irin abubuwan da suka wakana a lokacin da ake neman wanda zai zama abokin takarar Muhammadu Buhari gabanin zaben 2015.

Bukola Saraki ya ambato 'hana wasu zama abokan takarar Buhari' a matsayin daya daga cikin laifukan da suka sanya aka gurfanar da shi a gaban kotun da'ar ma'aikata a shekarar 2016.

Labarai masu alaka