Me ya sa 'yan Nigeria ke azarɓaɓin zuwa Turai ci-rani?

Yadda matasa ke mutuwa wajen ketara teku Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan ci-rani kan shafe kwanaki suna tafiya a cikin Sahara da teku don tsallakawa zuwa Turai

'Yan Nijeriya na daga cikin ƙasashen da hukumar kula da masu ƙaura ta ce na kan gaba-gaba cikin mutanen ƙasashen duniya da ke rawar jikin zuwa Turai don ci-rani.

Wakilin BBC Martin Patience ya gano cewa akasarin masu tafiya ci-rani daga Nijeriya na sanya ɗan-ba ne a jihar Edo.

Kelvin Emeson ɗan Nijeriya ne da aka izo ƙeyarsa daga Libya bayan jirginsu ya nutse a cikin teku, inda ruwa ya ci 'yar'uwarsa Augustina.

Ya ce jazaman ne na tari aradu da ka don cim ma burina na shiga Turai.

A cewarsa Augustina ma'aikaciyar jinya ce da ta yi aiki a wani ƙaramin asibiti don haka kuɗin da take ɗauka bai taka kara ya karya ba.

Mahaifiyarsu Charity wadda ta ce ba ta san lokacin da 'ya'yanta suka yanke shawarar yin wannan tafiya mai hatsari ba.

Mace mai ƙaramin ƙarfi don haka su Kelvin ke fafutukar neman hanyar samun kuɗin shiga don tallafa wa kansu da mahaifiyarsu.

A bana kadai, 'yan ci-rani masu yunƙurin zuwa ƙasashen Turai sama da dubu 40 ne suka tsallaka tekun Baharrum - kuma da yawa cikinsu 'yan Nijeriya ne.

Alkaluman da hukumar kula da ƙaura ta duniya ta fitar sun ce baya ga 'yan ƙasar Syria da Afghanistan, 'yan Nijeriya a yanzu sun dauki wani kaso mai yawa da ke ƙoƙarin yin bulaguro zuwa Turai.

Da yawa daga cikinsu sukan je Turai ne don neman aiki da rayuwa mai inganci - duk da yake, kasarsu ba ta fuskantar wani rikici.

Wani mai fataucin masu zuwa Turai a Edo, Friday Egwadoro ya ce ƙarancin karatu ne ya sanya shi shiga wannan harka.

Ya ce karon ƙarshe da ya yi fataucin wasu zuwa Libya ya ci karo da wasu ɗalibai da suka kammala digiri su uku a kan hanyarsu ta zuwa ci-rani Turai.

Labarai masu alaka