Gwamnatin Afghanistan za ta dandana kudarta - Taliban

Afghanistan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sojojin Afghan na fama da masu tada kayar baya na Taliban

Kungiyar Taliban ta bayar da sanarwar shiga lokacin kakar yake-yake, kwanaki kadan bayan mummun harin da suka kai wa dakarun Afghanistan.

Kungiyar ta ce za ta mai da hankali ne akan ''sojojin kasashen waje'' kuma za'a kai hare-haren ne ta hanyoyi daban-daban da suka hada da yakin sunkuru da kunar bakin wake da kuma amfani da sojoji.

Har yanzu kasar ba ta gama murmure wa daga harin da aka kai wa barikin rundunar sojoji a makon jiya ba.

Ga bayanai da jami'ai suka fitar, masu tada da kayar bayan su 10 ne suka shiga sansanin horar da sojoji a Mazar-e Sharif inda suka kashe akalla sojoji 135.

Wasu rahotanin sun nuna cewa yawan wadanda suka mutu ya haura hakan.

Ministan tsaron da shugaban rudunar sojoji ta kasar sun yi murabus bayan da aka kai harin.

Taliban ta yi barazanar cewa sojojin kasashen waje da ma na gwamnatin Afghanistan za su dandana kudarsu.

'Yan taliban sun ce kakar yake-yake ta wannan shekara za a sa mata suna Operation Mansouri domin tuna wa da shugabansu da Amurka ta kashe a wani hari ta sama.

Labarai masu alaka