Shugabancin Amurka na ba ni wahala —Trump

Shugaba Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Trump ya yi alkawura da yawa a lokacin yakin neman zabe

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana kewar rayuwarsa ta baya kuma yana mamakin yadda sabon aikinsa a fadar White House ke ba shi wahala.

Mista Trump ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "yana kewar rayuwarsa ta baya soboda yana da abubuwa da dama da zai yi a wannan lokaci."

Ya kara da cewa "wannan aiki na bani wahala fiye da rayuwata ta baya. Na yi tsammani aikin na da sauki".

Kusan babu wani lokaci da ya fi dacewa Mista Trump ya bayyana halin da yake ciki sama da yanzu.

Ya ce ''Ina kewar rayuwata ta baya".

Wani ya rubuta a shafin sada zumunta na Twitter cewa ''Na san yadda Mista Trump ke ji. Ni ma ina kewar rayuwata kafin a zabe ni.''

Jama'a da dama sun ta yi wa shugaban ba'a kan kalaman nasa.

Wasu kuma suka ce Mista Trump, wanda tsohon mai gabatar da shirin ne a Talbijin, na da abubuwa da yawa da zai koya.

A don haka suna ganin ya fadi gaskiya, kuma halayyarsa ta yin hakan abin koyi ne.

Akwai kuma wadanda suka yi tambayar cewa abu da zai zamo mai zafi ga Mista Trump shi ne idan wata rana majalisa ta yanke shawarar tsige shi saboda bukatunsa na kansa sun shiga harkokin gwamnati.

Labarai masu alaka