A karon farko malamai mata sun yi fatawa kan auren wuri a Indonesia

Women's Islamic conference in Indonesia Hakkin mallakar hoto BBC Indonesia
Image caption Taron ya hada jagororin mata Musulmai daga kasashe da dama

Manyan malaman addinin Musulunci mata sun gabatar da wata fatawa a kasar Indunisiya a kan aurar da kananan yara.

An gabatar da fatawar ne a karshen taron kwana uku da malamai mata a kasar suka gudanar, sai dai dokar ba ta zama wajibi a yi amfani da ita ba.

Malaman sun bukaci gwamnati da ta mayar da mafi karancin shekarun da za a yi wa mace aure su zama 18, ba shekara 16 ba kamar yadda suke a yanzu.

Mafi yawancin 'yan kasar Indunisiya Musulmai ne, kuma tana daya daga cikin kasashen da suke yawan aurar da kananan yara a duniya.

A cewar ofishin kula da kananan yara na Majalisar dinkin duniya, kashi daya ckin hudu na matan kasar ana aurar da su ne kafin su kai shekara 18.

An gabatar da taron ne a birnin Cirebon a kan tsibirin Java, wannan ne karo na farko da malaman addinin Musulunci mata suka shirya taro.

Mafiya yawan wadanda suka halarci taron 'yan kasar ne, sai dai an samu halartar wasu daga kasar Pakistan, da Saudiyya da ma sauran wasu kasashe.

Ana gabatar da Fatwa a kasar akai-kai, sai dai galibi majalisar malaman kasar ce suke gabatarwa, wacce ita ce hukuma ta koli a harkokin addinin Musuluncin kasar kuma dukkansu maza ne.

Fatawar ta kira aurar da kananan yara a matsayin "cutarwa" kuma ya zama dole a hana yin hakan.

Ninik Rahayu, wacce ita ce ta shirya taron, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Malamai mata sun san al'amuran da suka shafi mata da kuma abubuwan da suke kawo wa mata cikas, ba za mu jira har sai gwamnati ta zo ta kula da wadannan yara ba, muma za mu iya daukar mataki.

Malaman sun yi nazari inda suka gano cewa, yawancin kananan yaran da ake musu aure ba a barinsu su cigaba da karatunsu da sun fara sai ayi musu aure, daga karshe kuma a sake su.

Batun aurar da kananan yara na daya daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron, sauran sun hada da yi wa mata fyade da kuma lalata muhalli.

Labarai masu alaka