Hotunan Afirka a makon da ya gabata

Wasu daga cikin kyawawan hotunan Afirka da kuma wasu 'yan Afirka a ko ina a duniya.

Sapeur Hakkin mallakar hoto Tamasin Ford
Image caption Wasu matasa 'yan gayu daga DR Congo da Ivory Coast sun taru ranar Talata domin tunawa da mawaki Papa Wemba wanda ya mutu a bikin wakokin Femua a Abidjan shekarar da ta gabata
Sapeurs Hakkin mallakar hoto Tamasin Ford
Image caption Shi ne sarkin masu gayu, kuma shi ne ya samar da hadaddiyar kungiyar masu gayu.
Dan gayu Hakkin mallakar hoto Tamasin Ford
Image caption Dole dan gaye ya yi kwalliya da kyau, ya sanya kaya masu daukar hankali, su kuma sanya turare tare da gyara gashinsu.
Wata mata ke jiran masu saen kaya a titi streetside boutique a tsakiyan birnin cibiyar kasuwancin kasar wato Lagos Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata mata da ke sayar da gwanjon singileti, ke jiran masu saya a wata kasuwa da ke birnin Lagos ranar Laraba
Wani matashi kenan, ke tura Wul baro a kan titin Okepopo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani matashi ne nan ke tura Wul baro a kan titin Okepopo da ke birnin na Lagos.
Wata a tsaye cikin shagon ajiye kayan tarihin Kiristoci Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata mata ke zaune a wani shagon sayar da kayan tarihin Kiristoci lokacin ziyarar Fafaroma Francis zuwa birnin Alkahira, ranar Asabar.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan (Hagu)Tare da Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, ke wuce wani Abun girmamawa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan (Hagu)Tare da Shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, ke wuce wani abun girmamawa lokacin wata tarbar ziyara a birnin Ankara, da ke Turkiyya.
Wani mai tura Wul baro ke dakon wasu mayan robobi zuwa shagon mai sayar da su Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai tura Wul baro ke dakon wasu mayan robobi zuwa shagon mai sayar da su a wajen birinin Nairobi da ke kasar Kenya.
Mai goyon bayan jam'iyyar adawa a Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai goyon bayan Jam'iyyar 'Orange Democratic Party' a Kenya lokacin da aka kaddadamar da Raila Odinga a matsayin dan takarar hadin gwiwar Jam'iyyun adawa

Hotunan na kamfanonin dillancin labaran AFP, EPA, Getty Images and Reuters ne.

Labarai masu alaka